Kwamitin Duba Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara) ya karɓi waɗannan ƙudurori na majalisar dokoki da ke da nufin ƙirƙirar sabbin jihohi da ƙananan hukumomi.
JERIN SUNAYEN JIHOHIN da ake son karawa a Najeriya.
An karɓi kudurin karin Ƙirƙirar Sabbin Jihohi 31
Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulki, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisa a ranar Alhamis.
Ga jerin sunayen jihohin da aka gabatar da buƙatar ƙirƙirarsu a majalisar tarayya:
AREWA TA TSAKIYA
1. Jihar Benue Ala daga Jihar Benue ta yanzu.
2. Jihar Okun daga Jihar Kogi ta yanzu.
3. Jihar Okura daga Jihar Kogi ta yanzu.
4. Jihar Confluence daga Jihar Kogi ta yanzu.
5. Jihar Apa-Agba daga yankin Sanatan Benue ta Kudu.
6. Jihar Apa daga Jihar Benue ta yanzu.
7. Ƙirƙirar Jiha ta 37 wato Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
AREWA MASO GABAS
8. Jihar Amana daga Jihar Adamawa ta yanzu.
9. Jihar Katagum daga Jihar Bauchi ta yanzu.
10. Jihar Savannah daga Jihar Borno ta yanzu.
11. Jihar Muri daga Jihar Taraba ta yanzu.
AREWA MASO YAMMA
12. Jihar New Kaduna da Gurara daga Jihar Kaduna ta yanzu.
13. Jihar Tiga daga Jihar Kano ta yanzu.
14. Jihar Kainji daga Jihar Kebbi ta yanzu.
15. Jihar Ghari daga Jihar Kano ta yanzu.
KUDU MASO GABAS
16. Jihar Etiti a matsayin jiha ta shida a yankin Kudu Maso Gabas.
17. Jihar Adada daga Jihar Enugu ta yanzu.
18. Jihar Urashi a matsayin jiha ta shida a yankin Kudu Maso Gabas.
19. Jihar Orlu daga yankin Kudu Maso Gabas na Najeriya.
20. Jihar Aba daga yankin Kudu Maso Gabas na Najeriya.
KUDU MASO KUDU
21. Jihar Ogoja daga Jihar Cross River ta yanzu.
22. Jihar Warri daga Jihar Delta ta yanzu.
23. Jihar Bori daga Jihar Rivers ta yanzu.
24. Jihar Obolo daga Jihohin Rivers da Akwa Ibom.
KUDU MASO YAMMA
25. Jihar Toru-Ebe daga Jihohin Delta, Edo, da Ondo.
26. Jihar Ibadan daga Jihar Oyo ta yanzu.
27. Jihar Lagoon daga Jihar Legas ta yanzu.
28. Jihar Ijebu daga Jihar Ogun ta yanzu.
29. Jihar Lagoon daga Jihohin Legas da Ogun.
30. Jihar Ibadan daga Jihar Oyo ta yanzu.
31. Jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha daga Jihohin Ogun, Oyo, da Osun.
- Jihar New Kaduna daga Kaduna
- Jihar Gujarat daga Kaduna
- Jihar Tiga da Ari daga Kano
- Jihar Kainji daga Kebbi
- Jihar Etiti da Orashi a yankin Kudu maso Gabas
- Jihar Adada daga Enugu
- Jihar Orlu da Aba daga Kudu maso Gabas
- Jihar Ogoja daga Cross River
- Jihar Warri daga Delta
- Jihar Ori da Obolo daga Rivers
- Jihar Torumbe daga Ondo;
- Jihar Ibadan daga Oyo
- Jihar Lagoon daga Lagos
- Jihar Ijebu daga Ogun
- Jihar Oke Ogun/Ijesha daga Oyo/Ogun/Osun


Comments
Post a Comment